A baya bayan nan kasar Amurka na ci gaba da aiwatar da matakai daban daban, na shatile kamfanonin kasar Sin masu kirar ababen hawa dake aiki da lantarki. A kwanan nan ma gwamnatin Amurkan ta sanar da aniyarta ta gudanar da bincike kan irin wadannan ababen hawa da ake kerawa a kasar Sin, da nufin wai tabbatar da ba sa dauke da wasu abubuwa daka iya zama barazana ga tsaron kasa”.
Sanin kowa ne cewa Amurka ta mayar da batun “Tsaron Kasa” wani makami da take fakewa da shi wajen aiwatar da matakan baiwa kasuwar ta kariya, kana tana kago zarge-zarge marasa tushe, domin wanzar da manufarta ta danniya a fannin cin gajiyar fasahohi.
- Kotu Ta Tsare Mutane 29 Masu Rajin Kafa Kasar Yarbawa A Oyo
- Shari’ar Zargin Karkatar Da Dukiyar Al’umma: Ganduje Da Iyalansa Ba Su Halarci Kotu Ba
Ga duk mai bibiyar kafafen watsa labarai, ba zai rasa jin zargin da sakatariyar cinikayyar Amurka Gina Raimondo ta yi a baya bayan nan ba, cewa wai “ababen hawa kirar kasar Sin dake amfani da fasahohin zamani suna nadar bayanai daga matukansu, kana su aika su kasar Sin”.
Ko shakka babu wannan babban zargi ne da bai dace ya fito daga bakin babbar jami’i kamarta ba, kasancewar hakan zai zubar da mutuncinta, da na kasarta a idanun duniya, bayan da kowa ya gano cewa batun yunkuri ne kawai na shafawa kasar Sin bakin fenti.
Alal hakika, matakai daban daban da Amurka ke aiwatarwa a wannan fage, na sanya shingaye da siyasantar da harkokin tattalin arziki da cinikayya, na kawo tsaiko ga bunkasar masana’antun kera ababen hawa, tare da gurgunta tsarin shigar da su sassan kasuwannin duniya.
A matsayin Amurka na babbar kasa mai ci gaba, kamata ya yi har kullum ta rika martaba dokokin kasa da kasa a fannin hada-hadar tattalin arziki da cinikayya. Kana ta martaba yanayin takarar kasuwa bisa adalci. Kaza lika ta kauracewa hade komai karkashin manufar tsaron kasa, da nufin cimma muradun kashin kai, wato dai ta kauracewa “Fakewa da Guzuma Domin Harbin Karsana”.