A ranar Talata aka kunna wutar gasar Olympics da Birnin Paris ke shirin karba nan da ‘yan makwanni kuma bikin na gargajiya ya gudana ne a garin Olympia mai tsohon tarihi da ke Girka, matakin da ke nuna kai wa gabar karshe na shirye-shiryen da aka shafe shekaru bakwai ana yi kan gasar da za a fara a ranar 26 ga Yuli.
Jarumar fina-finan kasar Girka Mary Mina, da aka zaba a matsayin jagorar bikin gargajiyar ce ta kunna wutar Olympics din, gasar da karo na uku kenan da Faransa za ta karbi bakuncinta a Birnin Paris bayan hakan da ta yi a shekarun 1900, da kuma 1924.
- Sharhi: Kokarin Fahimtar Yanayin Tattalin Arzikin Sin Ta Bangarorin Ayyuka Guda 3
- Mun Damu Da Matsalar Yara ‘Yan Shila A Adamawa – Fintiri
Yayin jawabin da ya gabatar shugaban kwamitin shirya gasar Olympics na duniya Thomas Bach, ya ce ko shakkah babu mutane sun kosa a fara wasannin motsa jikin domin debe musu kewa daga tashe-tashen hankulan da suke karuwa da suka kunshi, ta’addanci da kuma munanan labarai.
A makon da ya gabata shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce za a bukaci Rasha ta tsagaita bude wuta a Ukraine yayin gudanar gasar ta Olympics, kamar yadda aka saba mutunta wasannin a lokutan baya, sai dai Rasha ta ki amincewa da tsarin bisa zargin cewa Ukraine za ta iya amfani da damar wajen sake kintsawa yakin da suke gwabzawa.
Barazanar Tsaro:
Amma kuma a karon farko shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce za a iya sauya kogin Seine, da aka tsara gudanar da bikin bude gasar Olympics da Birnin Paris zai karbi bakunci, zuwa filin wasa na Stade de France saboda barazanar tsaro.
Kwamitin shirya gasar ta Olympics da Birnin Paris zai karbi bakunci dai ya shiya gudanar da gagarumin bikin bude gasar a kogin Seine, da a tarihi ba a taba yin irinsa a wajen filin da za a gudanar da wasannin gasar.
To sai dai gasar ta zo ne a dai-dai lokacin da ake fuskantar rikici tsakanin Rasha da Ukraine da kuma Isra’ila da Hamas a Gaza, lamarin da ya sanya hukumomin Faransa suka ce bikin bude gasar na cika da fuskantar barazanar hari.
A zantawar da aka yi da shugaba Macron a ranar Litinin din nan, ya ce suna da mabanbantan tsare-tsare da za su iya maye gurbin gudanar da bikin bude gasar a kogin Seine.
Akwai dai kimanin mutum dubu dari 3 da aka tsara su kasance a wajen bikin bude gasar, da kuma karin wasu dubu dari 2 da za su kalli bikin bude gasar daga gine-ginen da ke kusa da kogin Seine.
Kawo yanzu dukkanin kasashen da za su halarci gasar sun amince da kasancewa a bikin bude gasar da za a yi a Seine, cikinsu kuwa har da Amurka da Isra’ila da suka fi fuskantar barazana.
Sai dai shugaba Macron ya ce za su yi dukkanin abin da ya kamata, don ganin an samu tsaro da zaman lafiya a yayin gasar kamar yadda aka saba a kowacce shekara da kasar take karbar bakunci.