Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na matukar nuna rashin gamsuwa, da bayyana adawa ga yadda wasu sassa ke dagewa, sai sun sauya batutuwa masu nasaba da Sin, da watsi da gaskiya, da gurbata gaskiya da karya, da kokarin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar ta Sin.
Yayin taron manema labarai na yau Litinin, wanda Wang Wenbin ya jagoranta, ya ce matsayar kasar Sin don gane da batutuwa masu nasaba da hakan a bayyana take. Kaza lika, hanya mafi dacewa da wanzar da zaman lafiya da daidaito a mashigin tekun Taiwan, ita ce ta kiyaye manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da nuna adawa da yunkurin “Samun ‘yancin Taiwan”.
- Me Ya Sa Ake Ganin Kasuwar Sin Tana Janyo Hankulan Kasa Da Kasa?
- Ministan Harkokin Wajen Gabon Ya Yabawa Nasarorin Da Gabon Da Sin Suka Samu A Fannonin Sada Zumunta Da Hadin Gwiwa
Wang ya ce, sakamakon hadin gwiwar Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN, an samu cikakken daidaito da zaman lafiya a yankin tekun kudancin kasar Sin baki daya, kuma babu wata matsala ga ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin. Kasar Sin ta rungumi manufar mayar da al’umma gaban komai, da cewa kamata ya yi ci gaba ya amfani dukkanin al’ummun Sinawa.
Jami’in ya kara da cewa, a halin da ake ciki, yankin musamman na Hong Kong na gaggauta cimma nasarar samun kyakkyawan jagoranci da walwala, yayin da yankunan Xinjiang da Xizang, ke kasancewa cikin yanayi na kyakkyawar zamantakewar al’umma, da wadata da daidaito, a gabar da kuma al’ummu kabilu daban daban ke rayuwa da aiki cikin zaman lafiya da wadatar zuci.
Wang ya ce, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma, Sin ta himmantu wajen yayata ci gaban bai daya na dukkanin kasashen duniya, yayin da kuma take mayar da hankali ga ci gaban kanta. Wasu bayanan bankin duniya, sun nuna cewa, gudummawar kasar Sin ga ci gaban tattalin arzikin duniya, ta dade da zarce wadda kasashe mambobin kungiyar G7 baki dayan suke bayarwa. (Saminu Alhassan)