A ranar Litinin ne rundunar sojin Nijeriya ta sallami wasu sojojinta biyu da aka kama da laifin satar wayoyin wutar lantarki (Armored cable) a matatar Dangote da ke Legas.
Matatar Dangote, an bude ta ne a ranar 22 ga watan Mayun 2023 a yankin Ibeju-Lekki na jihar Legas.
- Dakatar Da Ganduje: Alkalin Ya Yi Watsi Da Umurnin Da Ya Bayar
- Tsaro: Nijeriya Za Ta Karbo Jiragen Yaki 24 Daga Kasar Italiya
Ana sa ran matatar za ta iya sarrafa gangar danyen mai kusan ganga 650,000 a kowace rana.
An rahoto cewa, jami’an tsaro masu zaman kansu da wasu sojoji ne suka kama wadanda ake zargin, Kofur Innocent Joseph da Lance Kofur Jacob Gani.