Bayanai na baya-bayan nan sun nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2023, rarar man da ake iya hakowa a kasar Sin ta kai tan biliyan 3.85, wadda ta karu da kashi 1.0% idan aka kwatanta da makamancin lokacin a shekarar 2022, yayin da iskar gas da za a iya haka ya kai kyubik mita biliyan 6683.47, wanda ya karu da kashi 1.7% idan aka kwaranta da na makamancin lokacin a shekarar 2022. Wadannan alkaluma, sun jawo hankulan mutane sosai.
Bisa kididdigar da aka fitar a cikin sanarwar albarkatun kasa na kasar Sin na shekarar 2023 da ta rarar albarkatun mai da iskar gas ta kasa ta shekarar 2023, an gano yawan rarar sabbin albarkatun man fetur da iskar gas na kasar Sin na ci gaba da kasancewa a wani babban matsayi, ciki kuwa yawan sabbin danyen mai da aka gano, ya wuce tan biliyan 1.2 a cikin shekaru hudu a jere. (Bilkisu Xin)