An samu kimanin dala miliyan 28 na kudin shiga a cikin watanni 9, daga fiton kayayyakin da aka samar a yankin masana’antu na Kombolcha da Sin ta gina a Habasha.
Babban manajan yankin masana’antu na Kombolcha (KIP) Ahmed Seid, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar cewa, an samu kudin ne daga kayayyakin da aka samar a cikin yankin na KIP cikin watanni 9 na farkon shekarar kudi ta 2023/2024 da ake ciki yanzu haka a kasar Habasha, wadda aka fara daga ranar 8 ga watan Yulin 2023.
- Sin Ta Kalubalanci Amurka Da Ta Dubi Kanta Game Da Yanayin Kare Hakkin Dan Adam
- Sin Ta Yi Kira Ga G7 Da Ta Sauya Tsohuwar Halayyar Dora Alhaki Kan Wasu
Ahmed Seid ya kara da cewa, a cikin wannan lokaci, yankin na KIP ya samarwa mazauna sama da 850 guraben ayyukan yi.
Kamfanin gine-gine na kasar Sin na CCECC ne ya gina tare da kaddamar da yankin masana’antun na Kombolcha a watan Yulin 2017, a matsayin wani bangare na burin gwamnatin Habasha na bunkasa tattalin arzikinta da mayar da kasar zuwa cibiyar samar da kayayyaki a nahiyar Afrika. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)