Matatar man Dangote ta sanar da sake rage farashin man dizal da na man jirgi a kokarin saukaka farashinsa a sassan kasar nan.
Wannan na zuwa ne kasa da mako biyu bayan karya farashin farko da matatar mallakin attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote ta yi.
- An Kori Sojoji 2 Daga Aiki Kan Aikata Sata A Kamfanin Dangote
- Firaministan Sin Ya Jaddada Bukatar Kafa Managarcin Tsarin Kasuwar Jari
Sanarwar da matatar ta fitar, ta bayyana cewa daga yanzu za ta rika sayar da kowace litar man dizal a kan farashin Naira 940 sai kuma litar man jirgi akan farashin Naira 980.
Sanarwar ta bayyana cewa ragin farashin zai shafi masu cinikayyar da ke sayen litar man dizal miliyan biyar zuwa sama ne, yayin da abokan cinikayyar da za su sayi lita miliyan daya zuwa sama za su samu man dizal a kan farashin Naira 970.
Ragin farashin nazuwa ne yayin da ‘yan Nijeriya ke murna kan matakin farko na rage farashin man dizal ta yi daga Naira 1,200 zuwa 1,000.
Duk da cewa har yanzu farashin bai sauya a kasuwanni ba, amma akwai fatan matakin ya shafi yanayin hada-hadar kayayyakin da ake safararsu da man.
Matatar Dangote ta fara zaftare farashin dizal daga 1,600 zuwa 1,200, daga baya kuma ta sake yin ragi zuwa Naira 1,000, kafin daga bisani ta sake rage shi zuwa Naira 950.