Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar da ya zurfafa gyare-gyare da fadada bude kofa tare da rubuta na shi tarihi cikin aikin zamanantar da kasar Sin.
Xi Jinping ya bayyana haka ne a rangadinsa a Chongqing. Ya kuma kara da cewa, ya kamata Chongqing ya yi kokari wajen bunkasa ci gaba mai inganci da gina birnin zuwa wata muhimmiyar kafa ta raya yankin yammacin Sin a sabon zamani, haka kuma ya zama cibiyar bude kofa a yankin kan tudu.
- Mayakan Boko Haram 2 Sun Mika Wuya Ga Sojoji
- Sin Ta Kalubalanci Amurka Da Ta Dubi Kanta Game Da Yanayin Kare Hakkin Dan Adam
Da yake rangadi a cibiyar jigilar kayayyaki ta kasa da kasa dake Chongqing, shugaban ya bayyana bangaren jigilar kayayyaki a matsayin jijiyoyin tattalin arziki na hakika. Ya kuma bayyana cewa, ginin sabon yankin cinikayya na kan tudu zuwa teku, zai taimaka wajen inganta kara bude kofa a yankin na yammacin kasar Sin da ma yankunan kan tudu.
Xi ya kuma ziyarci tashar jigilar kwantainoni ta Chongqing, inda ya bayyana muhimmancin jigilar kayayyaki wajen ingiza ci gaban yankin na yammacin kasar Sin.
Haka kuma, bayan sauraron rahoto kan gina zagayayyen yankin tattalin arziki na Chengdu da Chongqing, Xi ya bukaci gwamnatin Chongqing ta mayar da hankali kan kirkire-kirkiren kimiyya da kuma bunkasa ci gaba mai inganci a fannin samar da kayayyaki. (Fa’iza Mustapha)