Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin Naira biliyan 1.2 duk wata don samar da tsaftataccen ruwan sha a cikin babban birnin jihar, kamar yadda kwamishinan albarkatun ruwa, Ali Makoda ya bayyana.
Makoda ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Laraba.
- Gwamnan Kano Ya Isa Amurka Domin Taron Tattaunawa Kan Kalubalen Tsaro A Arewacin Nijeriya
- Tarkunan Da Aka Dana Wa Ganduje A Kano
“Muna kashe Naira miliyan 400 a kowane wata wajen siyan dizal, Naira miliyan 387 wajen sayen sinadarai, yayin da kudin wutar lantarki ke kwashe Naira miliyan 280.
“Har ila yau, akwai sauran abubuwan kuma da ke lakume kudade. Muna iya kokari wajen gyara matsalar karancin ruwan sha a babban birnin jihar da kewayenta. Nan da kwanaki kadan, matsalar za ta zama tarihi,” in ji Makoda.
Makoda ya kuma dora laifin karancin ruwa a kan tsofaffin kayan aiki, musamman a cibiyar kula da ruwa ta Tamburawa da ke samar da ruwa ga mafi yawan sassan birnin Kano.