Gwamna Zulum Ya Bawa Yaro Dan Shekara 13 Tallafin karatu da zai lakume Naira Miliyan Biyar saboda Kwaikwayan gadar garin Maiduguri ta jihar Borno.
An gabatar da chek din kudi Naira Miliyan biyar na tallafin ilimi wanda gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da shi ga wata makaranta mai zaman kanta don amfanin yaron dan shekara 13, Musa Sani saboda amfani da kwababbiyar kasa, ya kwaikwayi gadar sama ta farko a jihar dake kusa da shataletalen Kwastan na Maiduguri.
An biya kudin ne ga Golden Olive Academy, Maiduguri domin daukar nauyin karatun yaron tun daga aji hudu na firamare zuwa kammala babbar Sakandare.
An haifi Musa ne a cikin wani gida mai karamin karfi da ke zaune a kewayen unguwar Gwange a Maiduguri, babban birnin jihar.
Gwamna Zulum ya yi mamakin hazakar yaron. Don haka Gwamnan ya tallafa wa yaron ta Bangaren karatu don yin amfani da basirarsa.