An kashe wani babban kwamandan sojoji a wani harin kwantan bauna da yammacin ranar Alhamis a jihar Katsina.
Lamarin dai ya faru ne a kauyen Malali da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, inda kwamandan wanda Manjo ne a rundunar sojin Nijeriya ya amsa kiran gaggawa.
- Atiku Ya Ziyarci Sanata Ningi, Ya Bukaci Majalisa Kar Ta Amince Da Zalunci
- Wuraren Bayar Da Tallafi Sun Zama Tarkon Mutuwa
A cewar wata ingantacciyar majiya, babban kwamandan na kan hanyarsa ne domin tallafa wa dakarun yankin da suka dakile harin ‘yan bindiga a lokacin.
“Yankin da ke kan titin Zangon Pawa, inda kauyen Malali yake, yana fama da matsalar ‘yan bindiga ”.
“Sauran jami’an soji da ke Malali ne suka nemi karin taimako daga sansanin Maraban Dan’Ali da ke kusa, nan da nan, Manjo ya yi gaggawar kawo dauki, inda a hanyarsa acikin motar Hilux ‘yan bindigar suka yi masa kwanton bauna suka kashe shi”. Inji wata majiya