Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa, Unai Emery ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da aiki a kungiyar har zuwa karshen kakar wasa ta 2027.
Emery ya koma Aston Villa cikin watan Nuwamban shekara ta 2022 bayan korar Ste-ben Gerrard, lokacin da kungiyar ke mataki na 16 a kasan teburin gasar Premier League ta Ingila.
- Sarkin Kano Ya Shawarci Ministan Sadarwa Kan Amfani Da Fasaha
- Yadda Liverpool Ta Ɓarar Da Damarta A Old Trafford
Mai koyarwar, mai shekara 52, ya ja ragamar kungiyar ta kare a mataki na bakwai a ba-ra, hakan ya sa ta samu gurbin Europa Conference League, kuma na farko a gasar Tu-rai tun 2010 zuwa 2011.
A kakar bana tana ta hudu a teburin Premier League, kuma dab take ta samu gurbin Champions League – ta bai wa Tottenham ta biyar tazarar maki shida, mai kwantan wasa biyu.
Aston Villa za ta samu gagarumar ci gaba idan Emery ya lashe Europa Conference League, sannan kuma idan kungiyar ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin Zakarun Turai na Champions League na badi.
Kawo yanzu Villa ta kawo karshen rade-radin da ake cewar watakila Bayern Munich ta yi zawarcin kociyan ko Liverpool, wadanda masu horar da su za su bar aikin a karshen kakar nan.
A kwarewar da Emery ke da ita ya kai Villa dab da karshe a Conference League, wad-da za ta kara da Olympiakos da fatan kai wa zagayen karshe a gasar Turai a karon far-ko tun 1982.
Emery ya lashe Europa League uku tare da SeVilla, ya kuma dauki daya a kungiyar Bil-larreal sannan ya horar da Arsenal watanni 18, wadda ya kai Arsenal mataki na biyar a teburin Premier League da kai wa wasan karshe a Europa League, inda Chelsea ta yi nasara.
Ya hada maki 115 a Premier League tun bayan da ya karbi aikin horar da Aston Villa, kociyan da suke gabansa, a wannan kwazon sun hada da na Manchester City da na Arsenal da kuma na Liverpool.