Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, a halin yanzu ta shirya tsaf don kaddamar da motoci 2,700 masu amfani da iskar gass a ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekarar, a daidai bikin cikar wannan gamnatin sheakra daya a kan karagar mulki.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, gwamnati za ta samar da tashoshin shan iskar gas din 100 a jihohi 18 na fadin tarayyar Nijeriya kafin karshen shekarar 2024.
- Matsalar Tsaro: Gwamnan Zamfara Ya Nanata Bukatar Amfani Da Fasahar Zamani
- ‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-18 Sun Shiga Tashar Binciken Samaniya Ta Kasar Sin
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman a kan harkokin yada labarai, Mista Bayo Onanuga, ya bayyana haka a takardar sanarwar da ya sanya wa hannun aka kuma raba wa manema labarai a Abuja ranar Lahadi.
“A karshen watan Mayu Nijeriya za ta fara daukar matakin shiga rukunin kasashen da suke amfani da motoci masu amfani da iskar gas a fadin duniya.
“An kammala dukkan shirye-shiryen da ya kamata na kaddamar da motoci masu amfani da iskar gas na farko a Nijeriya, za a yi bikin ne kafin cikar shugaba Tinubu shekara 1 a kan karagar mulki ranar 29 ga watan Mayu.,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, an shirya samar da motoci 600 a matakin farko da za a kammala a shekarar 2024.
A watan Oktoba na shekarar 2023, kusan wata 5 da janye tallafin man fetur shugaban Tinubu ya kaddama da kwamitin shugaban kasa don samar da motoci masu amfani da iskar gass don rage radadin janye tallafin man fetur da kuma bukatar samar da hanyoyin rage gurbacewa muhalli.
Shirin shugaban kasa na samar da motoci masu amfani da iskar gas miliyan 1 ba zai samu ba sai da hada hannun bangarori masu zaman kansu wadanda suka hada da kungiyoyin direbobi ta RTEAN, NARTO, da kuma NURTW, haka kuma ana neman hadin kan dukkan ‘yan Nijeriya don samun nasarar da ya kamata.