Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta shelanta cewa ta samu nasarar cike gibin da ta samu a zabubbukan baya, ta gudanar da Ingataccen zaben kujerar gwamna a jihar Osun da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.
INEC ta ce, hatta masu ruwa da tsaki a fannin siysar kasar nan, sun jinjinawa hukumar kan yadda ta yi kokari a wajen ayyukan ta a lokacin zaben, musamman yadda kayan zaben suka isa rumfunan gudanar da zaben a kan lokacin da ya dace.
Festus Okoye, Kwamishina a Hukumar kuma shugaban kwamitin samar da bayanai da kuma wayar da kan masu karbar katin zabe ne ya bayyana hakan a hirarsa da gidan talabin na Channels.
Yaci gaba da cewa, mun koyi darussa da dama daga zaben Kujerar Gwamna na jihar Ekiti wanda hakan ya bamu damar inganta zaben na jihar Osun.
A cewarsa, mun kara samun ci gaba wajen tura kayan aiki a kan lokacin da ya dace, mun tura kayan aikin zabe na jihar Osun tun karfe 7:30 na safe zuwa rumfunan da za a yi zaben.
Kwamishinan ya ce, muna son mu kammala yin rijistar masu katin jefa kuri’a a kan lokaci don mu tabbatar da sahihan yawan wadanda aka yiwa rijista.