Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya ce Gwamnatin Tarayya na bukatar zuba jarin dala biliyan 10 a duk shekara, domin farfado da harkar wutar lantarki na tsawon shekaru 10 masu zuwa.
Adelabu ya bayyana haka ne a Abuja ranar Litinin, a wajen wani zaman bincike na kwana daya kan kudurin dakatar da karin kudin wutar lantarki da hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya (NERC) ta yi amma kwamitin majalisar dattawa kan samar da wutar lantarki ya shirya bincike kan lamarin.
- Mamu Ya Nemi A Dauke Shi A Hannun DSS Zuwa Gidan Gyara Hali Na Kuje
- JAMB Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar 2024, Sakamako 64,624 Na Karkashin Bincike
“Domin a farfado da wannan fanni, gwamnati na bukatar kashe kasa da dala biliyan 10 a duk shekara nan da shekaru 10 masu zuwa.
“Hakan ya biyo bayan abubuwan da ake bukata na samar da ingantaccen kayan aiki a fannin, amma gwamnati ba za ta iya daukar wannan nauyi ba.
“Don haka, dole ne mu sanya wannan fannin ya zama abin sha’awa ga masu zuba jari da masu ba da lamuni.
“Domin mu jawo hankalin masu zuba jari, da masu bada lamuni, dole ne mu sanya fannin ya yi kyau, kuma hanya daya tilo da za a iya samar da hakan, ita ce, a sanya farashin kasuwa a fannin” in ji shi.