Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Kashim Shattima ya bayyana cewa zabo mu-tane 100 da suka ba da gudummuwa a rayuwarsu da aka ba su lambar yabo a ci-kinsu har da matattu da rayayyu, wannan babban darasi ne ga al’umma.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a matsayinsa na babban bako, wanda Malam Musa Aliyu Magajin Malam Jahun ya wakilta a taron da kungiyar ceto al’ummar Nijeriya (DHS), wanda ya gudana a jami’ar Bayero da ke Jihar Kano.
- Naira Za Ta Ci Gaba Da Farfadowa, in ji Shettima
- An Gurfanar Da Mutane 2 A Kotun Sojoji Kan Harin Tudun Biri
A wurin taron, an dai bai wa fittatun mutane lambar yabo wanda suka hada da malamai, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa, masana da sauransu, wadanda suka ba da gudummuwarsu wajen ci gaban al’ummar Nijeriya.
Daga cikin dimbin mutattun mutanen da suka samu lambar yabo da addu’ar alkairi bayan sun koma ga Allah, akwai sheikh Nasiru Kabara, Khalifa Isyak Rabiu, Malam Aliyu Akilu, fitaccen mawallafin wakokin Hausa da na addini, Marigayi Malam Bala Kalarawi, Marigayi Sheik Mahmuda Adam da sauransu.