Sabon zababben gwamnan jihar Osun a inuwar Jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke, ya Karyata rade-radin da ake yadawa cewa ministan kula da harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya taimaka masa lashe zaben Kujerar Gwamna a jihar.
In ba a manta ba, an zabi Adeleke a matsayin sabon gwamnan jihar ne a makon da ya gabata, bayan da gwaman jihar mai ci, Gboyega Oyetola na Jam’iyyar APC ya sha kaye a hannun Adeleke.
An dai yi ta yin hasashen cewa, rashin jituwar dake tsakanin dan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu da Aregbesola ne ya janyo APC mai mulki a a jihar ta sha kasa a lokacin zaben gwamnan na jihar Osun.
Amma Adeleke a martanin da ya mayar a hirarsa da gidan talabijin na Channels ya ce sam bawata ganawa ta musamman dake tsakaninsa da Minista Aregbesola kafin gudanar da zaben a jihar.
Sai dai ya aminta da cewa wasu abokan siyasar ministan sun hada kai da shi wajen samun nasarar sa akan Oyetola.