Matashiyar mai sayar da dafaffiyar zogale a kwaryar birnin tarayya Abuja, Fatima Mai Zogale ta samu tagomashi da alheri tun bayan da shahararren mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya wake ta bayan da ya ci zogalar da take sayarwa a kwanakin baya.
Matashiyar wadda ta ce ita yar asalin Akilibu ce da ke Jihar Kaduna a Arewa maso yammacin Nijeriya ta fara sana’ar sayar da zogale a karkashin wata uwar dakinta a wurin da Yahuza Suya a Abuja, inda anan ne ta hadu da mawakin wanda ya ji dadin zogalan da ya saya a wajenta har ya wake ta.
- Babu Inda Mayaudara Da Mahassada Suka Taru Kamar Masana’antar Kannywood – Adam Zango
- Ni Na Yi Ruwa Da Tsaki Har Ali Nuhu Ya Samu Shugabancin Hukumar Fina-finai Ta Nijeriya – Rarara
Bayan wakar ta fito ne uwar dakinta ta sallameta daga aiki saboda abinda ta kira amfani da zogalan da bata ta wajen tallata kanta kamar yadda ita Fatima ta fadawa manema labarai.
Korar da aka yi mata daga inda take sayar da zogale ne ya sa mutane suka tausaya mata daga cikinsu akwai Rarara wanda kuma shi ne ya yi mata wakar da ta janyo mata hakan, inda ya yi alkawarin tallafa mata da jarin da za ta ci gaba da sayar da zogalarta a Abuja.
A wata hira da yayi da manema labarai Rarara ya bayyana sunayen wasu daga cikin manyan mutane a Nijeriya da suka yi alkawarin bayar da wani abu domin Fatima ta samu damar ci gaba da gudanar da kasuwancinta cikin aminci.