Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga matasa na wannan sabon zamani da su yi kokarin rubuta babinsu na kurciya wajen daukar nauyin zamanantar da kasar Sin.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa ga matasan kasar Sin, gabanin ranar matasa ta kasar Sin, wadda ta fada ranar Asabar.
Xi, a madadin kwamitin kolin JKS, ya mika sakon taya murna ga matasan kasar baki daya.
Xi ya ce, a cikin sabuwar tafiya a wannan sabon zamani, matasan kasar Sin na dukkan kabilun kasar Sin sun kasance a matsayin “jagorori kuma muhimman runduna” a fannoni daban daban, kamar su kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da farfado da yankunan karkara, da bunkasa muhalli mara gurbata, da hidimar zamantakewa, da kare kasa bisa kiran jam’iyya da jama’a. Xi ya kara da cewa kwamitin kolin JKS yana da cikakken aminci da kuma kyakkyawan fata ga matasa. (Mai fassara: Yahaya)