A ranar Lahadi ne gwamnatin jihar Legas ta yi nuni da cewa, za ta rushe dakuna fiye da 100 da ke karkashin gadar Adeniji Adele daga ranar Litinin.
Kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa, Tokunbo Wahab ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi.
A cewarsa, hukuncin na zuwa ne bayan karewar wa’adin sa’o’i 48 da aka ba duk mazauna dakunan da su kwashe kayayyakinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp