Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin magance tsadar magunguna domin samun sauki ga ‘yan Nijeriya.
Darakta-Janar ta Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), Farfesa Mojidola Adeyeye, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi a Abuja.
- An Shawarci NAFDAC Ta Bullo Da Dabarun Fasaha Wajen Yaki Da Jabun Magunguna
- Hukumar NAFDAC Ta Bankado Magunguna Marasa Rajista Na Naira Miliyan 15 A Abuja
Sanarwar ta bayyana cewa Adeyey ta ba da wannan tabbacin ne a wata lacca ta yanar gizo da jaridar The Cable ta shirya, domin murnar cika shekaru 10 da kafuwa, mai taken: “Maganin farashin magunguna”.
A cewar Adeyeye, tsadar magunguna da ake yi a kasar nan zai zama tarihi domin hukumar na hada guiwa da masana’antun harhada magunguna domin rage farashin magunguna.
Ta bayyana farfado da masana’antar harhada magunguna ta cikin gida a matsayin maganin tsadar magunguna a kasar.
Daraktar ta ce, magungunan da ake samarwa a cikin gida za su fi samun sauki da araha idan aka kwatanta da magungunan da ake shigowa daga waje idan aka farfado da masana’antar harhada magunguna ta cikin gida.
A cewarta, raguwar darajar Naira ya fi tsadar kayan da ake samarwa a cikin gida saboda hauhawar farashin kayayyaki ya sa sayo kayan da ake shigowa da su don samar da su suka yi tsada sosai.
Ta ce, saboda wahalar da ke tattare da sayan dala, farashin magungunan da ake shigowa da su daga kasashen waje ya kai kololuwa.
Adeyeye ta kuma bayyana cewa hukumar ta NAFDAC karkashin jagorancinta ta fara shirin “5 plus 5” wanda ya shafi kamfanonin shigo da magungunan da masana’antun harhada magunguna na cikin gida za su iya samar da su don samun sabuntawa na tsawon shekaru biyar.
Ta ce a cikin shekaru biyar na sabuntawar, dole ne mai shigo da kaya ya yi ƙaura zuwa masana’antu na cikin gida ko kuma ya yi haɗin guiwa da masana’antun cikin gida.
Ta ce sama da kashi 30 cikin 100 na sabbin kamfanoni a Nijeriya sun samo asali ne sakamakon shirin “5 plus 5”, inda ta kara da cewa hakan ya bai wa masu damar shigo da kaya kwarin guiwar gina kamfanoninsu.
Adeyeye ta jaddada cewa wasu tsare-tsare na hukumar NAFDAC na rage tsadar magunguna, inda ta kara da cewa masana’antun cikin gida ba za su iya farawa ba tare da karfafa tsarin doka ba.