Da safiyar yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da shugabar kwamitin kungiyar EU Ursula von der Leyen a fadar Elysee ta kasar Faransa, bisa gayyatar da aka yi masa.
Xi Jinping ya bayyana cewa, ziyararsa a kasar Faransa ita ce ziyarar aiki ta farko da ya yi a kasar waje a bana, kuma ganawar bangarorin uku ta zurfafa ma’anar ziyararsa ta wannan karo. Ya ce kasar Sin tana duba dangantakar dake tsakaninta da kasashen Turai bisa manyan tsare-tsare da ka’idar hangen nesa, inda ya ce dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai na da muhimmanci ga kasar Sin a fannin raya dangantakarta da kasashen duniya, bisa salonta na musamman da kuma matsayinta na wata babbar kasa, kuma, kasashen Turai su ne muhimman abokan kasar Sin, yayin da take kan hanyarta ta neman zamanintar da kanta. Ya kara da cewa, Sin tana fatan dangantakar dake tsakaninta da kasar Faransa da ma sauran kasashen Turai za ta kasance ta taimakon juna da neman ci gaba cikin hadin gwiwa.
Bugu da kari, shugaba Xi ya ce, a wannan lokaci da duniya ke fuskantar sauye-sauye, kamata ya yi kasar Sin da kasashen Turai su hada kansu da yin shawarwari cikin hadin gwiwa, domin inganta dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata, tare da ba da gudummawa wajen raya kasashen duniya cikin zaman lafiya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)