Gwamnatin jihar Adamawa ta rufe makarantun gwamnati da na masu zaman kansu sakamakon barkewar Annobar cutar kyanda a jihar.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwar da babbar sakatariyar ma’aikatar Ilimi da ci gaban jama’a ta jihar, Aisha Umar, ta rattabawa hannun ranar Litinin a Yola.
- Gwamnatin Katsina Ta Ɗauki Ma’aikata 304 Don Kula Da Zirga-zirgar Ababen Hawa A Jihar
- Shettima Zai Je Amurka Don Halartar Taron Kasuwanci Tsakanin Amurka Da Afirka Na 2024
Sanarwar ta ce, an dauki matakin rufe makarantun ne da nufin dakile yaduwar cutar da kuma baiwa hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar (PHCDA) damar yi wa Yara kanana allurar rigakafin kamuwa da cutar.
A cewar sanarwar, “ma’aikatar Ilimi tana mai sanar da ranar Litinin mai zuwa, 13 ga Mayu, 2024, a matsayin sabuwar ranar da za’a sake bude makarantun.
“Don haka ma’aikatar Ilimi ta umurci dukkanin makarantun gwamnati da na masu zaman kansu da su rufe makarantu.”
Akalla yara 42 ne hukumomi a jihar suka tabbatar da cewa, sun mutu sakamakon barkewar annobar a jihar Adamawa.