Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a kasar Hungary, a ranar 8 ga wata bisa agogon kasar ne, aka yi bikin kaddamar da wani shirin talabijin da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya tsara, mai suna “Labarun Da Xi Jinping Ya Fi So”, a Budapest na kasar Hungary. Inda tsohon shugaban kasar Pál Schmitt, da tsohon firaministan kasar Péter Medgyessy suka taya murnar kaddamar da shirin.
Daga ranar 8 ga wata ne aka fara gabatar da shirin a gidan talabijin na Hungary da wasu manyan kafofin yada labaru na kasar.
Shi ma shugban CMG Shen Haixiong, da shugaban asusun goyon bayan kafofin yada labaru da kula da dukiyoyi na Hungary Dániel Papp sun kaddamar da shirin tare a wajen bikin. (Tasallah Yuan)