Shahararren dan wasan kwallon kafar Faransa wanda yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain, Kylian Mbappe ya bayyana a wani faifan bidiyo da ya dora a shafinsa na X cewa wannan shekarar ita ce shekararsa ta karshe a PSG.
Mbappe, wanda ya koma PSG daga kungiyar kwallon kafa ta Monaco a kan kudi har Yuro miliyan 180 a 2017, ya zama daya daga cikin manyan ‘yan wasa da ake tunkaho da su a harkar kwallon kafa a duniya.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 30 Da Wani Malami A Zamfara
- Umarnin CBN Na Cire Harajin Tsaron Intanet Ya Tayar Da Kura
Ya jefa kwallaye fiye da 250 a wasanni 300 da ya buga wa PSG, inda ya lashe manyan kofuna da suka hada da gasar Ligue 1 da French Cup cikin shekaru bakwai da ya shafe a kungiyar.
Real Madrid ta jima tana son daukar dan wasan, wanda ake rade-radin zai koma kungiyar a karshen kakar wasanni ta bana.
Mbappe wanda dan asalin kasar Faransa ne, an jima ana alakanta shi da Real Madrid, lamarin da ya sanya alaka ta yi tsami tsakanin Madrid da PSG a kan dan wasan.