Tarihin masana’antar Kannywood ba zai cika ba sai an saka sunan Fati Muhammad,wadda tana daya daga cikin tsoffin jaruman da suka taka rawar gani wajen ganin masana’antar ta tsaya da kafafunta a daidai lokacin da take rarrafe.
Fatima Muhammad ta fara harkar fim a shekarar 2000, wanda a wancan lokacin ta fito a manyan fina-finai da suka hada da Sangaya, Marainiya, Babban Gari da sauransu, ba za a taba mantawa da rawar ganin da Fati ta taka a tarihin Kannywood ba.
- Shugaba Xi Ya Jaddada Muhimmancin Cimma Sabbin Matakai A Fannin Yada Ilimin Akidu Da Siyasa
- Masu Masana’antu Na Kasar Sin Sun Raba Fasahohinsu A Majalisar Dinkin Duniya
- Rukayya Dawayya
Rukayya Dawayya wadda sunanta ta karade koina musamman masu sha’awar kallon fina-finan Hausa tun a shekarar 2000 inda ta fara fitowa a cikin shirinta mai suna Dawayya, jarumar wadda ta fito a fina finai fiye da 150 ta samu tagomashi a tsakanin masoya wadanda ke fatan kallon fina finanta a kodayaushe.
Shaharar da Rukayya Dawayya ta yi musamman a arewacin Nijeriya ya sa ta zamo daya daga cikin manyan jarumai masu samun tallace tallace daga manyan kamfanoni, haka zalika jarumar tana hadawa da siyasa a cikin manyan al’amura da ta saka a gaba.
- Jamila Nagudu
Jamila Umar wadda aka fi sani da Jamila Nagudu na daya daga cikin manyan jarumai mata a masana’antar Kannywood wadanda Allah ya zubawa basira wajen nishadantarwa da ilimantarwa ta hanyar fina finanta,tana kuma daya daga cikin jarumai mata wadanda suka shafe shekaru da dama ana damawa dasu a cikin masana’antar.
Jarumar ta fito a manyan fina finan masana’antar Kannywood da suka hada da Indon Kauye, Ruwan Dare, Jamila Da Jamilu da sauransu, Jamila ta fito a fina finai fiye da 200 a tarihi haka kuma ta samu kyaututtuka da dama a wannan fage nata na jarumar Kannywood.
- Hadiza Aliyu Gabon
Jaruma Hadiza Aliyu Gabon wadda akafi sani da Gabon a takaice ta zama daya daga cikin manyan jarumai mata da masana’antar Kannywood take alfahari dasu tsawon shekaru, daga wani kauye kusa da birnin Librebille zuwa Kano, daga malamar makarantar Firamare zuwa jarumar fina finan Hausa Hadiza Gabon ta taba lashe kyautar gwarzuwar Kannywood a farkon shekarunta na fara harkar fim.
Hadiza ba a fina finan Kannywood kawai ta tsaya ba, ta tsallaka har zuwa kudancin Nijeriya inda ta fito a wasu fina finan Nollywood, ta samu tallace tallace daga manyan kamfanoni a Nijeriya da suka hada da MTN, Glo da Dangote.