Kasashen Sin da Amurka, za su gudanar da tattaunawa ta farko ta manyan jami’an gwamnati, kan kirkirarriyar basira wato AI, a ranar 14 ga watan Mayu a birnin Geneva na kasar Switzerland. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan hadduran dake tattare da fasahar da batun tafiyar da harkokin duniya da sauran batutuwan dake jan hankalin bangarorin biyu. (Fa’iza Mustapha)