Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta raba kayan tallafin ga ‘yan gudun hijira 24,000 da ɓarnar ‘yan bindiga ta shafa a ƙananan Hukumomin Jibiya da Mani da ke Jihar Katsina.
Kayan tallafin da hukumar ta raba sun haɗa da abinci, buhunan shinkafa masu nauyin kilogiram 10 guda 13,000, da katan na tumatir 120, da katan na sinadarin ɗanɗanon girki 120, da jarkunan man girki mai cin lita 20 guda 120 da kuma buhunan gishiri mai nauyin kilogiram 20 guda 120.
Da yake jawabi a yayin rabon kayan, Darakta Janar na NEMA Mustapha Habib Ahmed wanda Babban Jami’in Bayar da Tallafi da Tsugunarwa na Hukumar a Shiyyar Arewa Maso Yamma da ke Kaduna, Kasimu Muhammad Jere ya wakilta, ya yi bayanin cewa tallafin wani ɓangare ne na taimakon da NEMA ke bayarwa a madadin Gwamnatin Tarayya domin rage wa mutanen da suka rasa matsugunansu raɗaɗin da suke ji.
A jawabinsa a madadin Gwamnatin Jihar Katsina, Babban Daraktan Hukumar Bayar da Tallafin Gaggawa ta Jihar (SEMA), wanda wani Darakta a hukumar, Yunusa Mahuta ya wakilta, ya yaba wa NEMA bisa karamcin da ta yi, tare da isar da godiyar gwamnatin jihar.
Da yake mayar da jawabi a madadin ‘yan gudun hijira a Ƙaramar Hukumar Mani, ɗan majalisar da ke wakiltar yankin a Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Alhaji Aminu Ashiru Mani ya yi godiya ta musamman ga NEMA bisa bayar da tallafin.
Har ila yau, shi ma wani shugaban al’umma da ya yi magana a madadin ‘yan gudun hijira na Ƙaramar Hukumar Jibiya, Alhaji Kabiru Mashe, ya gode wa Gwamnatin Tarayya bisa yadda ta dube su da idon rahama ta hannun NEMA.
Tallafin kayan dai na NEMA an raba wa ‘yan gudun hijira da ke garuruwan Shimdiɗa, Garin Mai Wuya, Tsambe, Garin Zango da Kwari da ke Ƙananan Hukumomin Jibiya da Mani a Jihar Katsina.