A farkon makon nan, fadar White House ta Amurka, ta sanar da sabbin matakan kariyar cinikayya kan kamfanonin fasahohi masu tsafta na kasar Sin, ciki har da ninninka harajin ababen hawa kirar kasar Sin masu aiki da lantarki da ake shigarwa Amurka zuwa kaso 100 bisa dari.
Ko shakka babu, wannan mataki ne da ya fi kama da farfagandar siyasa, duba da cewa an dauke shi ne a cikin shekarar babban zaben kasar, ko alama bai yi kama da mataki mai la’akari da tsarin kyautata tattalin arziki ba.
- Shugabannin Sin Da Rasha Sun Tattauna Da Juna
- Kasar Sin Ta Bayyana Rashin Gamsuwa Da Karin Haraji Da Amurka Ta Yi
Masharhanta da dama na cewa, harajin baya ma da Amurka ta kara kan irin wadannan kayayyaki zuwa kaso 25 bisa dari, ya riga ya kore irin wadannan nau’o’in motoci daga shiga Amurka. To amma da karin na baya, da wanda aka sanar a ’yan kwanakin nan, ba abun da za su haifar sai koma baya ga Amurka a fannoni da dama, kuma ko kadan wannan mataki na kokarin dakile ci gaban sashen makamashi mai tsafta na Sin, ba zai taimakawa Amurka ta bunkasa nata masana’antun fannin ba.
Da farko dai, matakan za su hana Amurkawa cin gajiya daga ababen hawa masu rahusa, masu amfani da tsaftacaccen makamashi. Kaza lika hakan zai hana su amfana daga takarar kasuwa, tare da tursasa su sayen ababen hawa masu matukar tsada.
Ko da a bangaren masana’antun sarrafa karafa ma, a shekarun baya bayan nan, matakan da Amurka ta rika dauka na kariyar cinikayya, ba su taimakawa kasar da komai ba, matakan ba su dakile raguwar guraben ayyukan yi ba. Maimakon haka, sai ma kara tsadar hajojin kamfanonin fannin suka haifar, da takaita kyakkyawar takara ga kamfanonin na Amurka, daga karshe hakan ya illata tattalin arzikin kasar.
Manazarta dai na ganin maimakon kakkaba shingen cinikayya, kamata ya yi ’yan siyasar Amurka su amince da muhimmancin rungumar takara mai tsafta, su karfafa gwiwar kirkire-kirkire da bude kasuwanni, ta yadda takara za ta kai ga samar da sauki, da bunkasar tattalin arzikin dukkanin sassa, idan kuma ba haka ba “Kaikayi zai koma kan mashekiya”. (Saminu Alhassan)