Babu shakka samamayen da hukumar Hisba ta kai unguwar Kwanar Danbukari a ranar Lahadi, 5 ga Mayun 2024, a cikin birnin Katsina da zummar tayar da masu kidan DJ da aka gayyoto a wajen wani ya haifar da zazafar mahawara, musamman a kafafen yada zumunta na zamani.
Wannan farmaki da hukumar Hisba ta kai ya yi sanadiyar rasa ran, Malam gambo Mai Faci, wanda aka yi zargin harsashi ne ya taba shi lokacin da jami’an C-Watch da suka rako hukumar Hisba domin tarwatsa DJ da kuma kamashi idan an samu sa’a.
- Jami’ar FUBK Ta Gudanar Da Bikin Ɗaukar Sabbin Ɗalibai 2, 217 A Kebbi
- Hajjin Bana: Saudiyya Ta Kaddamar Da Kundayen Wayar Da Kai Ga Mahajjata Cikin Harsuna 16 Har Da Hausa
Ana iya cewa, wannan dai shi ne karon farko da ita wannan hukuma da Gwammna Malam Dikko Umar Radda ya kafa bayan hawansa mulki, da ta kai farmaki irin haka kuma har aka samu asarar rai guda daya tare da jikkata wasu da dama.
Jama’a da dama dai sun yi tofin Allah wadai ga ayyukan wannan hukuma da take cewa ita aikin Allah take yi, sai gashi ta fara aikin nata da kashe dattawa da kuma raunata bayin Allah saboda masu DJ.
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa an shirya yin zanga-zanga a ranar Juma’ar da Malam Gambo ya rasu, don nuna fushi da kin amincewa da abin da hukumar Hisba ta yi, sai dai batun ya gamu da cikas bayan da wasu dattawan suka ce a bar wa Allah komi.
Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana cewa, a ranar Lahadin aka yi biki a unguwar Kwanar Danbukari, wanda ana ciki shagalin biki sai ga jami’an hukumar Hisba sun zo domin hana wannan biki, sakamakon haka hatsaniya ta tashi, kuma jami’an C-Watch da suka rako Hisba suka yi harbi.
Baba shakka wannan harbi ya bar baya da kura, mausaman yadda ake yada labaran cewa hukumar Hisba ta yi harbi, jama’a da dama sun yi mamaki yadda za a ce hukumar irin ta Hisba ta yi amfani da bindiga wajen tarwatsa taro mai makon yin nasiha da lalama kamar yadda suke ambatawa cewa, Hisba aikin Allah take.
Bayan wannan harbi da aka yi, Malam Gambo wanda aka ce yana sana’ar faci a kusa da inda wannan lamari ya afku, an garzaya da shi zuwa asibitin koyarwa ta Jihar Katsina domin yi masa magani, kuma a iya zaman sa a can kafin Allah ya dauki ransa hukumar Hisba ce ta dauki nauyin yi masa magani.
Wani abu ya fusata jama’a shi ne, yadda kafafen sada zumunta na zamani suka ruwaito wani mutun da aka ce shi ne jami’in hulda da jama’a na hukumar Hisba na cewa ba harbin Malam Gambo aka yi ba, duwatsu ne da jama’a suka rika jefawa a lokacin yamutsin ya same.
Ko shakka babu hakan bai yi wa jama’a da dama dadi ba, musamman iyalansa da ‘yan’uwa da kuma abokan arziki, sannan lokacin da Allah ya yi masa rasuwa ba a ga shugaban hukumar Hisba ba a wajen jana’iza da kuma gaisuwa, wanda hakan tasa jama’a ke cewa ya kamata a bi kadin wannan bayan Allah domin ganin an bi masa hakkinsa na kisan da aka yi masa babu hakki.
Daga Bangaran Hukumar Hisba Ta Katsina
Bayan wadannan zarge-zarge da kuma maganganu da jama’a ke yi, wakilinmu a Jihar Katsina ya samu tattaunawa da baban Kwamadan Hukumar Hisba na Jihar Katsina, Dakta Aminu Usman (Abu Ammar) domin jin ta bakinsa da kuma matsayarsa kan wannan lamari.
Dakta Usman ya fara da yin ta’aziya ga iyalan marigayi Malam Gambo da ‘yan’uwa da mutanen Jihar Katsina, inda ya yi addu’ar Allah ya jikansa ya karbi bakuncinsa ya sanya wannan al’amari ya zame masa sanadiyar shiga Aljanna.
Haka kuma ya yi tambihi kan wadanda suka rika yin rubuce-rubuce lokacin faruwar wannan al’amari. Ya ce da yawa daga cikin mutane ba su fadin gaskiyar abin da ya faru, suna fadin san zuciyarsu domin cimma wata manufa tasu.
“Hukumar Hisba ba ta rike makami, doka ba ta ba mu iznin rike bindaga ba, hatta hotan wani dan hisba da ake yadawa rike da bindiga a kafafen sadarwa na zamani, ba da izninmu ya yi hotan ba, kuma shi ma ya tabbatar, sannan yanzu haka mun dauki mataki kansa,” in ji shi.
Dakta Aminu ya fadi yadda abin ya faru, inda ya ce suna zaune a ofis wani mutun daga unguwar Kwanar Danbukari ya buga masa waya cewa gashi ana DJ kuma jama’ar unguwar ba sa so, amma yaran sun ki tashi, saboda haka ya turo ‘yan hisba su tashe su.
Ya kara da cewa umarnin da ya ba da na idan za a tafi wannan samame a tafi da jami’an C-Wacth, saboda shirin da aka ce masu DJ sun yi. Ya ce kadda a harbi kowa idan an samu turjiya a harba bindaga sama, sannan a kwaso kayan DJ idan an samu mai DJ din a kamo shi, wannan shi ne umarnin da ya ba da.
Sai dai har yanzu Dakta Aminu bai amince cewa harbin da aka yi wa Malam Gambo ne ya yi sanadiyar mutuwarsa ba, yana mai cewa binciken likita ya tabbatar da cewa ba a harbi Malam Gambo ba, jifa ce ta same shi, ba harbin bindiga ba kamar yadda ake yadawa.
A cewarsa, tun daga lokacin da wannan al’amari ya faru gwamnatin Jihar Katsina ta hannun hukumar Hisba ne suke daukar nauyin yi masa magani, kuma ko bayan Allah ya yi masa rasuwa sun kai kayan abinci gidansa tare da wasu kudade domin yin cefane.
Dakta Aminu ya ce abin da ya hana su zuwa ta’aziyya da kuma jana’iza shi ne, jama’an tsaro suka ba da shawara cewa kadda su je domin yadda jama’a suka fusata da hukumar Hisba, domin wani abu na iya faruwa idan suka je a daidai wannan lokaci.
Sai dai ya ce bayan abubuwa sun lafa, sun samu ganawa da iyalan mamacin, inda suka bayyana cewa sun yafe, sun bar wa Allah ba sa neman diyya a wajan gwamnati.
Ya ce wannan dalilin ya sa Gwamna Radda ya yi alkawarin bai wa ‘ya‘yan Malam Gambo guda biya aikin gwamnati tun da sun yi karatu, sannan akwai mace wanda za a ba ta jari domin yin sana’a.
Haka kuma ya nuna takaicinsa kan irin yadda wasu mutane suka rika amfani da wannan damar wajen ruruta wutar al’amari maimakon kamawa a kashe ta, yana mai cewa babu shakka a sanadiyar kai wannan farmaki da hukumar Hisba ta yi ne ya yi sanadiyar rasuwa Malam Gambo, saboda komai yi riga ya faru, kuma ya yi alkawarin cewa haka ba za ta sake faruwa a wannan hukuma tasu ba.
“Sai dai ina mai shaida wa al’umma cewa ba wai aikin Hisba ya zo karshe bane, maganar tsaftace al’umma a Jihar Katsina yanzu aka fara, saboda haka yana sanar da jama’a su ji tsoron Allah su bar duk abin da Allah ya hana domin ta haka ne za su samu fahimtar juna da jama’a. Ina rokon Allah ya kare faruwar haka a nan gaba”