Jam’iyyar APC mai mulki ta gabatar da tsohon gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi wa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu takarar mataimaki a zaben 2023 a ranar Laraba a hukumance.
Hadimin shugaban kasa kan sabbin kafafen sadarwa, Bashir Ahmad ne, ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter.
- INEC Ta Mayar Wa Davido Martani Kan Bai Wa Adeleke Takardar Shaidar Lashe Zabe
- Yawan Tashar Sadarwa Ta 5G Da Sin Ta Gina Ya Kai Kusan Miliyan 2
Ahmad ya ce “Jam’iyyar mu ta APC ta gabatar da Kashim Shettima a matsayin mataimakin dan takararmu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
“Bola Tinubu ya dauko Shettima a matsayin mataimakinsa ne bayan da ya lashe zaben fidda-gwanin APC na shugaban kasa.”
Sai dai, bayan Tinubu ya zabo Shettima an samu suka daga wasu jihohin kasar nan, inda akasarin ‘yan Nijeriya suka nuna sha’awar son a daukar Kirista a matsayin mataimakin na Tinubu.