Kungiyar hadin gwiwa da raya tattalin arziki ta duniya, da kwamitin kungiyar tarayyar Turai EU, sun daga zaton bunkasuwar tattalin arzikin Sin a bana da kashi 0.2 cikin dari. Kana kamfanin ba da shawara kan harkokin kamfanoni da kasuwa na Kearney, shi ma ya gabatar da rahoto game da kamfanonin da sassan kasa da kasa suka fi zubawa jarin kai tsaye, inda ya shaida cewa, Sin ta inganta matsayinta daga na 7 a bara zuwa na 3 a shekarar bana, inda ta zama ta farko a jerin sabbin kasashe mafiya bunkasar tattalin arziki a duniya.
A ranar 17 ga wannan wata, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da bayanin yanayin tattalin arzikin kasar na watan Afrilu, wanda ya yi daidai da zaton da sassan kasa da kasa suka yi wa kasar ta Sin. Yawan bunkasuwar masana’antun kasar Sin ya karu da kashi 6.7 cikin dari bisa na makamancin lokaci a bara, adadin da ya karu da kashi 2.2 cikin dari kan na watan da ya gabace shi.
- Shugabannin Matan APC Na Neman Ganduje Ya Kara Wa Mata Yawan Gurabe
- Zanga-zangar Karin Kudin Wuta: Gwamnati Ta Shelanta Matakin Da Za Ta Dauka
Kaza lika zaton ayyukan kamfanonin kasar ya zama cikin yanayi mai kyau, kana yawan harkokin cinikin sha’anin samar da hidimomi, shi ma ya zama cikin yanayi mai kyau a watanni hudu a jere, kuma dukkan kididdigar da aka fitar na shaida cewa, an raya tattalin arzikin Sin yadda ya kamata, da kiyaye samun farfadowa.
Har ila yau kuma, yawan cinikin waje na kasar Sin, ya nuna kyakkyawan fata ga duniya. A watan Afrilu, yawan kayayyakin shige da fice na kasar Sin ya karu da kashi 8 cikin dari, bisa na makamancin lokacin bara, kana yawan cinikin shige da fice daga watan Janairu zuwa Afirlun bana, ya kai matsayin koli bisa na makamantan lokutan da suka gabata.
A daya hannun kuma, bisa yanayin raunin farfadowar tattalin arzikin duniya, cinikin shige da fice na kasar Sin, ya kara imanin sassan kasa da kasa a fannin zuba jari a kasar Sin. Kamar yadda wasu shugabannin kamfanonin kasashen waje suka fada, kasar Sin dake inganta tattalin arziki yadda ya kamata, ta ba da tabbaci ga kamfanonin waje, da su aiwatar da hada-hadarsu a cikin kasar. (Zainab Zhang)