Kwararriyar Likitar mata, Dakta Blessing Babaji, ta yi kira ga mata, musamman masu ciki; don mayar da hankali kan zuwa awo asibiti, don duba lafiyarsu da kuma ta jariran da suke dauke da su.
A cewarta, awo ga mata masu ciki, wani tsararren abu ne da ake yi don kulawa da lafiyar mace mai ciki da kuma dan da take dauke da shi har zuwa lokacin da za ta haihu.
- Noman Aya Da Yadda Yake Samar Da Kudin Shiga
- Bunkasuwar Tattalin Arzikin Sin Ya Kara Imanin Sassan Kasa Da Kasa Game Da Kasar
“Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya, ta tsara cewa; a duk yayin da mace ke dauke da ciki, wajibi ne ta je awo duk bayan mako hudu har lokacin da cikin nata zai kai wata bakwai, sannan kuma bayan ya kai wata takwas; za ta rika zuwa duk bayan mako biyu, yayin kuma da ya shiga wata na tara; za ta rika zuwa wannan awo a kowane mako.”
Har ila yau, a lokacin wannan awo; ana yin gwaje-gwaje da dama ga mai ciki, domin duba lafiyarta da kuma ta dan da ke cikinta.
Gwaje-gwajen da ake yi a lokacin awo sun hada da kamar haka: 1- Gwajin jini: Ana gwada jinin mace mai juna biyu, don duba yawansa; idan akwai wata matsala a ba ta magani, don ta samu isasshen jinin; ita da dan da ke cikinta.
2- Ana duba fitsarin mai juna biyu, domin duba yiwuwar kamuwa da ciwon siga ko wani abu makamancinsa.
3- Ana kuma duba nauyin mai juna biyun da tsayinta, don tabbatar da cewa; ba za ta samu matsala a lokacin haihuwa ba.
Haka zalika, awo yana da matukar muhimmanci da amfani ga lafiyar mace mai juna biyu da kuma jaririn da ke cikin cikinta, domin kuwa da zarar an ga wata damuwa; za a yi kokarin daukar matakin da ya dace ba tare da wani bata lokaci ba, in ji Daktar.