Barkan mu da sake haduwa a cikin shirin namu na Ado da Kwalliya. Yau shafin zai zo muku da yadda ake yin kitso kala-kala na zamani. Amma a kashin farko, za mu yi bayani a kan irin wanda ake ce wa ‘Fulani Style’.
Abubuwan da za ki tanada
Kibiya, abin taje kai (comb), man gashi.
Yadda ake yi
Da farko dai akwai kalolin kitso da yawa na zamani. Ga kuma yadda za a yi kitson. Da fari za ki taje kan sai ki shafa man kitso domin ya sa miki laushin gashi. Za ki raba gashin kan ki gida biyu daga tsakiya ya zamo rabi sama rabi kasa.
Bayan kin raba su gida biyu sai ki fara kitsa rabin na kasa daya daya wanda aka fi sani da Bob Marley, har sai kin karasa shi zuwa karshe. Rabin na sama kuma sai ki kara raba shi gida biyu daga tsakiya amma gefe da gefe. Zai zama hagu da dama kennan, sai ki yi kitso irin na ‘All back’ yadda zai rufe Bob Marley din kasa. Amma daga gefen wurin kunne za ki bar gashin da zai yi kitso guda daya ko biyu, sai ki kitsa shi zuwa gaba, haka za ki yi wa na dayan gefen. Za ki iya saka bead ko wani abin kwalliya ko ki bari haka.