• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Jigawa Umar Namadi Ya Raba Kayan Makaranta 30,000 Ga Dalibai Mata

by Abubakar Sulaiman
1 year ago
Jigawa

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ƙaddamar da rabon riguna 30,000 ga ɗalibai mata a manyan makarantun sakandire da ke faɗin jihar. Taron rabon ya gudana ne a makarantar sakandiren kimiyyar mata ta gwamnati da ke Jahun, wanda ma’aikatar ilimi mai zurfi ta shirya.

Gwamna Namadi ya jaddada fifikon da gwamnatinsa take bayarwa kan ilimin yara mata, wajen samar da kayan sawa kyauta. Ya kuma bayyana cewa ilimi ga ƴaƴa mata a Jigawa kyauta ne tun daga matakin firamare zuwa manyan makarantu, inda ya nuna muhimmancin ilimi ga al’umma.Gwamnan ya kuma yi alkawarin inganta hanyoyin samun ilimi mai sauƙi da inganci.

  • Ramadan: Gwamnatin Jigawa Za Ta Ciyar Da Mutum 171,900 A Kullum Da Azumi – Namadi
  • Obi Na Jam’iyyar Labour Ya Yi Wata Ganawar Sirri Da Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido

Namadi ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samar da yanayi mai kyau na ci gaban malamai, tare da himmatuwa wajen ci gaba da ba da horo da sake horarwa don inganta ayyukan koyo da koyarwa.

Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Jigawa Malam Isa Yusuf,  ya yabawa gwamnan bisa wannan shiri da yayi domin zai taimaka wajen zaman ɗalibai mata a makarantu. Ya ƙara da cewa gwamnan ya amince da gyara makarantun mata guda 12, da raba littafan motsa jiki 70,000, da kuma sayo injinan dinki domin taimakawa dalibai su samu sana’o’i daban-daban.

Ɗalibai a aji yayin ɗaukar darasi a Jigawa
Ɗalibai a aji yayin ɗaukar darasi a Jigawa

Shugabar ƙungiyar ANCOPSS ta jihar, Asmau Sulaiman, ta godewa gwamnan bisa tallafin da yake ba wa yara mata a fannin ilmin ƴaƴa mata, ta yadda kowace yarinya a Jigawa za ta iya zuwa makaranta.

LABARAI MASU NASABA

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Wasu daga cikin Waɗanda suka ci gajiyar shirin Safiya Danladi da Zainab Ibrahim sun bayyana godiyarsu tare da yin alƙawarin daukar karatunsu da muhimmanci.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

gombe
Ilimi

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma
Ilimi

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
ASUU
Ilimi

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Next Post
Masana Sun Yabawa Rawar Da Sin Ke Takawa Wajen Inganta Ilimi A Afrika

Masana Sun Yabawa Rawar Da Sin Ke Takawa Wajen Inganta Ilimi A Afrika

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.