Asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND) ya bayyana cewa, dalibai a manyan makarantun gwamnatin tarayya ne za su cike bayanansu na bukatar lamuni a rumbun tattara bayanai na Asusun.
Babban Jami’in Asusun, Akintinde Sawyerr, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron wayar da kai ga tsarin bayar da lamunin a Abuja.
- Aikin Hajji 2024: NAHCON Ta Kwashe Maniyyata 7,582 Don Sauke Farali
- Ƴansanda Sun Kashe Ƴan Bindiga 2 Sun Ƙwato Bindigu 2 da Alburusai
Sawyer, ya ce, ɗalibai waɗanda makarantunsu suka dora bayanansu a kan manhajar Asusun ne kadai za su cancanci neman lamunin.
“A ranar 24 ga Mayu, 2024 ne za a bude kashi na farko na dalibai masu neman tallafin karatu da ke karatu a makarantun tarayya kamar su Jami’o’i da Kwalejojin Kimiyya da Kwalejojin ilimi da kwalejojin fasaha, wadanda cibiyoyinsu suka kammala dora bayanan dalibansu a manhajar Asusun, don neman samun lamunin.” In ji Sawyer