Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya, sun dakile wani yunkurin sace mutane a Abuja, inda suka kubutar da wasu da aka yi garkuwa da su.
Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar, ta ce hakan ya biyo bayan sasame da dabaru kan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai garin Dawaki a ranar 19 ga watan Mayu, 2024, da misalin karfe 11:30 na dare.
- Ƴansanda Sun Kashe Ƴan Bindiga 2 Sun Ƙwato Bindigu 2 da Alburusai
- Peter Obi Ya Ziyarci Waɗanda Suka Ƙone A Masallaci A Kano
Ta ce jami’an rundunar ‘yansandan Abuja karkashin jagorancin kwamishinan ‘yansanda, CP Benneth C. Igweh, sun yi gaggawar kai dauki yankin.
“Bayan nuna jarumta da hadin kai, ‘yansanda tare da hadin gwiwar mafarauta, sun kai wa maharan farmaki, tare da yi musu kwanton bauna a tsaunin Ushafa da ke Bwari da tsaunin Shishipe da ke Mpape.
“Hakan ya kai ga yin barin wuta na tsawon lokaci, lamarin da ya tilasta musu tserewa da raunukan harbin bindiga daban-daban, sannan aka ceto wasu da aka sace.
“Daya daga cikin wadanda aka ceto na kwance a asibiti inda ake kula da lafiyarsa, yayin da kwamishinan ‘yansandan Abuja, CP Benneth C. Igweh, ya kara tabbatar da shirin rundunar na samar da zaman lafiya da tsaro a yankin.“