Wani sakamakon bincike na jin raayin alumma, da jaridar The Guardian ta Amurka ta wallafa a baya bayan nan, ya nuna yadda duk cikin Amurkawa biyar, daya daga cikinsu ke ganin abu ne mai kyau, a cimma burin siyasa ta hanyar tarzoma.
Ko shakka babu hakan abun tsoro ne, da tayar da hankali, ganin cewa wannan tunani ya yi hannun riga da ainihin tushen dimokaradiyya, wanda ya tanadi cimma duk wani buri ta maslaha da kwanciyar hankali.
Wani abun lura game da wannan bincike, shi ne yadda Amurkawa ke saurin yarda da farfagandar ’yan siyasa, wadda ke haifar da rashin yarda, da nuna kyama, da amincewa daukar matakan tada zaune tsaye, yayin da suke son cimma wani buri na siyasa ko zamantakewa.
Ko da yake dai Bahaushe kan ce Barewa ba za ta yi gudu dan ta ya yi rarrafe ba. Duniya ta ga misalin irin wannan tunani tun daga kan jagororin Amurka, inda alal misali, a ranar 6 ga watan Janairun shekarar bara, daruruwan magoya bayan tsohon shugaban kasar Donald Trump, suka yi kutse cikin ginin majalissar dokokin kasar na Capitol, da nufin hana bayyana tsohon shugaban kasar a matsayin wanda ya sha kaye a babban zaben da ya gabata.
Wanda hakan ya sabbaba rasuwar mutane 7 da jikkatar gwamman mutane. Masu bibiyar lamarin sun tabbatar da cewa shi kansa tsohon shugaba Trump, ya nuna wasu alamu na goyon bayan wancan kutse.
Masharhanta dai na ganin idan har wannan yanayi na yin watsi da tushen dimokaradiyya ya ci gaba da kamari a Amurka, mai yiwuwa kasar ta fuskanci manyan bore masu nasaba da siyasa a nan da ’yan shekaru masu zuwa.
Domin kaucewa hakan, wajibi ne jagororin kasar su yi karatun ta-nutsu, su yi hangen nesa wajen wayar da kan Amurkawa, game da illar dake tattare da daukar doka a hannu, da kin amincewa da mabanbantan raayoyi, da nuna isa, wadanda dukkaninsu munanan dabiu ne da ka iya haifarwa kasar da maras ido.
Uwa uba kuma, ya zama wajibi gwamnatin Amurka ta dawo daga rakiyar manufarta ta shiga sharo ba shanu, da nuna karfin tuwo ga sauran kasashe, ko nuna kyama ga hanyoyin ci gaba da sauran kasashe suka zabawa kan su, domin kuwa irin wannan tunani ne ke haifarwa ’yan kasar ta yanayi na kangarewa, da kin karbar gaskiya!