Hukumar Kwastam da ke Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta samu nasarar kwace kwayar tramadol 54,000 da allurorin kayan maye da kasusuwan jaki da naman jaki da sauran wasu kayayyaki da aka yi fasakaurinsu da kudinsu ya haura sama da naira biliyan 3. 1 a sassa daban-daban da ke a shiryar.
Kwantirolan shiyyar, Ahmadu Bello Shuaibu ya sanar da hakan a taron manema labarai a shalkwatar hukumar da ke Kaduna.
- NDLEA Ta Kama Wani Fasinja ÆŠauke Da Kwayar Tramadol 4,000 A Filin Jirgin Sama Na Legas
- Kwastam ta Mika Jabun Dalar Amurka Da Jirage Marasa Matuka 148 Da Ta Kwace Ga EFCC Da Sojoji
Bello ya ce hukumar ta yi wannan nasarar ce daga ranar 17 ga watan Afrilu zuwa ranar 17 ga watan Mayun 2024, inda kuma aka cafke mutane 4 da ake zargi.
Wannan shiyyar na hukumar ta hadada da Kaduna, Kano, Jigawa, Katsina, Zamfara, Sakkwato, Kebbi, Neja, Kogi, Kwara da kuma Abuja.
Bello ya ci gaba da cewa, kwayar ta tramadol, jami’an shiyyar ne suka kama kayan bayan samun bayanan sirri a ranar 2 ga watan Mayun 2024, kan babbar hanyar Saminaka zuwa Nimbiya da kuma Kafanchan da ke a Jihar Kaduna.
Ya kara da cewa, kayan an yi safafarsu ne a cikin wata mota don a kai wa ‘yan bindiga da ke a dajin Saminaka na karamar hukumar Lere da ke a jihar Kaduna.
Haka zalika, ya ce, a ranar 25 ga watan Afirilun 2024, bayan samun bayanan sirri jami’an shiyyar sun kama wata babbar mota mai lamba GGE 526 DL a babbar hanyar Sakkwato zuwa Gusau da ke a Jihar Zamfara dauke da haramtattun kaya.