A wani gagarumin biki na tsakar dare, maimartaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shiga fadar mulkin Kano mai ɗimbin tarihi da karfe ɗayan daren yau Asabar.
Hakan ya biyo bayan mayar da shi a hukumance da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a ranar Juma’a, bayan rusa masarautu guda biyar da tsohon gwamna yayi tare da maido da masarautar Kano kamar yadda take kafin shekarar 2019. Mataimakin gwamnan jihar da jami’an gwamnatin ne suka raka Sanusi II fadar da misalin ƙarfe 1:30 na safe.
- Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
- Sarki Biyu A Gari Ɗaya: Aminu Ado Ya Isa Kano
Wannan matakin na bikin tsakar daren ya biyo bayan wani yunƙurin shirin komowa da ake zargin hamɓararren sarki Aminu Ado Bayero ya ke yi, wanda baya gari a lokacin da aka yanke hukuncin tsige shi a jihar.
Sarki Aminu wanda aka naɗa shi a matsayin Sarkin Bichi a shekarar 2019 sannan kuma ya zama Sarkin Kano na 15, tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya tsige Sunusi Lamido II a shekarar 2020. Matakin da Gwamna mai ci a yanzu Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na mayar da Sanusi II na nufin ya yi watsi da dokar da gwamnati Ganduje ta yi kenan ta rarraba masarautar Kani 5, inda ya yanzu gwamnan ya mayar da Sanusi II a matsayin Sarki tilo a jihar.
Duk da zaman ɗar ɗar da ake ciki Sarki Aminu ya koma Kano a safiyar yau Asabar inda magoya bayansa suka tarɓe shi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano. Magoya bayansa sun yi ta rera waƙoƙi da addu’o’i na goyon bayansa.
Zuwansa Kano ya sa gwamnan jihar bayar da umarnin kama shi don zai haifar da hargitsi a jihar.
Mataimakin gwamnan Kano Comr. Aminu AbdulSalam ya bayyana cewa akwai hannun mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro a cikin yunƙurin dawo da Sarki Aminu Ado kan karaga.