Rundunar ‘yansandan jihar Jigawa ta kama wani mutum mai kimanin shekara 33 mai suna Mahdi Salisu a karamar hukumar Taura, wanda aka zarginsa da laifin zama hamshakin dilan miyagun kwayoyi.
Labarin kamun ya bayyana ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda na jihar Jigawa DSP Lawan Shiisu Adam ya bayar ga manema labarai babban birnin jihar da ke Dutse.
Dubun Mahadi Salisu, ta cika ne, lokacin da, lokacin da ‘yansanda suka yi dirar mikiya a kan guraren za suke zargin ana aikata laifuka.
Majiyarmu ta shaida mana cewa, kwamishinan ‘yansandan jihar ya umarci dukkan dukkan DPO din da ke dinga kai farmaki maboyar masu laifi sau biyu a kowane mako.
Ya ce, “kai wa yi wa dillalyn kwayoyin mai suna Mahdi Salisu a Bakin Kasuwa, ya biyo bayan wani rahoton sirri ne da jami’an ‘yansandan suka samu daga garin Taura, na cewa, an ga wanda ake zargin da kullin tabar wiwi guda dari da biyu da kuma tabar wiwi kunshe a cikin wata bakar leda, wadanda kuma suka nuna a matsayin shaida.
Shiisu ya ci gaba da cewa, binciken wanda ake zargin, ya haifar da kama wadansu mutane wadanda su ma ake zarginsu da hada baki wajen aikata laifi.
Saboda haka, ya ce, dukkan wadanda aka Kaman za gurfanar da su gaban kotu, bayan kammala bincike.
Kwamishinan ‘yansanda na jihar Jigawa Aliyu Sale Tafida, ya gargadi dukkan masu aikara laifuka da su yi wa kansu kiyamul laili su bari, tun kafin su shiga hannu.