Malaman addinin Musulunci a Jihar Kano sun yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya bai wa al’ummar jihar damar magance rikicin masarautar ba tare da amfani da karfin iko ba.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin samar da zaman lafiya a jihar.
- Gwamnatin Tarayya Ta Fara Gina Gidaje Masu Saukin Kudi 1,250 A Jihohi Hudu
- Jami’an Tsaro Na Ganawar Sirri Da Abba Da Sarki Sanusi II A Fadar Kano
Malaman sun bayyana matukar damuwarsu dangane da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a masarautar, inda suka bukaci Gwamnatin Tarayya da ta sa baki domin wanzuwar zaman lafiya.
A cikin wata sanarwa da Shaikh Abdullahi Uwais Limanci ya sanya wa hannu, malaman sun yi gargadin cewa lamarin na iya haifar da tashin-tashina.
Sanarwar ta kara da cewa “Jihar Kano na daya daga cikin jihohin da aka fi samun zaman lafiya a Nijeriya duk da sarkakiyar siyasarta, ya zama wajibi shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauki dukkan matakan da suka dace domin wanzar da zaman lafiya a jihar.”
Malaman sun jaddada muhimmancin barin al’ummar Kano wajen warware matsalolinsu cikin ruwan sanyi, ba tare da yin amfani da karfi ba wanda a cewarsu hakan zai iya haifar da asarar rayuka.
Sun bayyana muhimmancin tattaunawa da mutunta juna wajen tunkarar rikicin da ke faruwa a yanzu.
“Muna kira ga mai girma shugaban kasa da ya bai wa al’ummar Jihar Kano damar magance wadannan matsaloli cikin ruwan sanyi ba tare da yin amfani da karfi da zai kai ga asarar rayuka da dukiyoyi ba.
Gammayar kungiyar malaman ta kuma yi kira ga bangarorin sarakunan da ke rikici da juna da su yi amfani da hanyoyi da suka dace don sim zaman lafiya a tsakaninsu.
Malaman sun yi alkawarin shiga tsakani tare da tuntubar duk bangarorin da abin ya shafa don samar da mafita cikin lumana.
A halin yanzu dai al’amura sun fara daidaita a jihar, bayan da shugaban hukumomin tsaro a jihar suka gana da duka bangarorin biyu da suka hada da tsagin sabon Sarki Sanusi Lamido II wanda ke samun goyon bayan gwamnati mai ci.
Sai kuma tsagin tsohon Sarki Aminu Ado Bayero, wanda wasu rahotanni suka bayyana yana samun goyon baya daga sama.