Rundunar Ƴansandan jihar Sakkwato ta tabbatar da kisan gilla ga wata mata mai matsakaicin shekaru a wani Otal dake garin Sakkwato.
A wata tattaunawa da wakilinmu, kakakin rundunar ASP Ahmed Rufai ya tabbatar da faruwar mummunar ƙaddarar ga Bazawarar, wacce bincike ya tabbatar tana da ƴaƴa huɗu.
- Ina Nan A Matsayin Sarkin Kano, Har Sai Na Ga Umarnin Kotun – Sanusi II
- Matsayar Ƙungiyar Sarakunan Arewa A Tsaya Kan Umarnin Kotu Kan Rikicin Sarki 2 A Kano
ASP Rufai ya ce, “An samu gawar marigayiyar ne a cikin mummunan yanayi na yankan Rago a ɗakin Otal ɗin.
Tuni dai Ƴansanda suka fara binciken lamarin, kuma ana zargin tare suka zai da wanda ya kashe ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp