Mai shari’a, Amina Adamu Aliyu ta babbar kotun Kano da ke zamanta a kan titin Miller, ta hana ‘yansanda da hukumar tsaro na farin kaya (SSS) da sojojin Nijeriya daga tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da aka maido.
Sarkin ya shigar da karar ne tare da masu nada Sarkin Kano da suka hada da Madakin Kano, Yusuf Nabahani; Makaman Kano, Ibrahim Sarki Abdullahi; Sarkin Bai, Mansur Adnan da Sarkin Dawaki, Maituta Bello Tuta.
- Wata Sabuwa: Kotu Ta Hana Aminu Ado Da Sauran Sarakuna 4 Kiran Kansu Sarakuna A Kano
- Sojoji Sun Sake Bude Kasuwar Banex A Abuja
Da take bayar da wannan umarni, Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta kuma tsinkayar da jami’an tsaro daga duk wani nau’in muzgunawa ko kama Sarkin da masu nada Sarkin.
An dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga Yuni, 2024.
Mun rahoto muku cewa, Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta bayar da umarnin korar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga karamar fadar Nassarawa a jiya Litinin.