Jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun cafke daya daga cikin kasurguman ‘yan bindigar da suka addabin jama’a musamman a cikin Jihar Zamfara wanda aka fi sani da suna Baleri.
A ranar Talata ne runduna ta musamman da ake kira ‘’Farautar Bushiya” ta cafke Balari da wasu dimbin yaransa a garin Tankama da ke yankin Gidan Runji a Jihar Maradi daf da iyakar Nijeriya da Nijar.
- An Kashe Masunta 31, 40 Sun Yi Ɓatan Dabo A Wani Harin ‘Yan Ta’adda A Borno
- An Kashe Mutane 5000, An Sace 7000 Cikin Shekara 1 A Mulkin Tinubu – Bincike
Jami’an tsaron sun kai samame ne a Rugar Kowa Gwani bayan da suka samu bayanan sirri da ke cewa ‘yan bindigar dauke da makamai sun tattaru a wannan kauye.
Lokacin da yake gabatar da ‘yan bindigar a gaban mahukunta, babban kwamandan rundunar ta ‘’Farautar Bushiya’’ Kanar Mohamed Almoctar Niandou, ya ce za su ci gaba da jajircewa domin tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasashen biyu.
Baleri, ya kasance daya daga miyagun ‘yan bindigar da suka addabin jama’a musamman a Jihar Zamfara, sannan daya daga cikin baraden da kasurgumin dan bindigar nan Bello Turji ke alfahari da su wajen kai hare-hare da kuma yin garkuwa da mutane musamman a yankin Arewa maso Yammaci.
Kimanin wata daya da ya gabata, jami’an tsaron Jamhuriyar Nijar sun yi nasarar cafke wani dan bindigar mai suna Kachalla, tare da tasa keyarsa zuwa Yamai domin ya fuskanci shari’a.