Shugaba Bola Tinubu, ya ce gwamnatinsa tana cika alkawurran da ta yi wa al’ummar kasar nan yayin yakin neman zabe.
Tinubu wanda ya taya ‘yan Nijeriya murnar cika shekaru 25 kan mulkin dimokuradiyya, ya kuma nemi hadin kan al’umma domin samar da kyakkyawar kasa da za ta zamo abin alfahari ga kowa.
- NAHCON Ta Gargadi Alhazai Kan Shiga Da Haramtattun Kayayyaki Saudiyya
- Shugaba Xi Ya Yi Kira Da A Zamanantar Da Ayyukan Tsaron Al’umma
Tinubu ya kuma yi gargadi kan jefa dimokuradiyya cikin mawuyacin hali yana mai cewa “Dole mu ci gaba da hada kai wajen gina kasarmu da kuma jaddadawa a koda yaushe, b mu da inda da ya fi Nijeriya.’’
A wani jawabi da ya yi wa majalisar dokoki, Tinubu ya nemi hadin kan ‘yan majalisar da ma sauran jama’ar wajen ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatinsa da kuma bunkasa Nijeriya.
Shugaban ya kuma nemi goyon bayan majalisar wajen kammala aiki a kan kasafin kudin da ya gabatar mata, wanda ya ce zai taimaka wajen aiwatar da tsare-tsaren da gwamnati ke da su, masu muhimmanci ga jama’ar kasa.