Tsohon shugaban kasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya caccaki manufofi da tsare-tsaren gwamnatin Shugaban kasa, Bola Tinubu kan lamuran da suka shafi tsaro da tattalin arziki, yana mai cewa, gwamnati mai ci ba ta daura turbar tafiyar da harkokin mulki yadda ya kamata ba.
Baro-baro ya bayyana cire tallafin man fetur wanda ya janyo cikas wajen huldar kai tsaye tsakanin ‘yan kasuwancin canjin da kuma canjin kudaden kasar waje a hukumance, gami da tsoma baki dumu-dumu kan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar da ke makwafta da Nijeriya, wato Jamhuriyyar Nijar.
- Rikicin Masarautar Kano: Lauyoyi Da Alƙalai Sun Tozarta Ɓangaren Shari’a – Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi
- Sojojin Nijar Sun Cafke Kasurgumin Dan Bindigar Da Ya Addabi Zamfara
Obasanjo ya lura kan cewa matakai uku da gwamnatin Tinubu ta dauka, biyu daga ciki sun kasance kusan ma wajibi ne a dauki matakin hakan, amma wajen aiwatar da su ne aka tafka kurakuran da suka jefa sashin tattalin arzikin kasar cikin halin ni-‘yasu.
Ya kuma bayyana cewar kasar nan ba za ta kai zuwa matakin da ake fatan zuwa ba har sai shugabanninta sun bijiro da ajandan ci gaba na tsawon shekara 25 da dokar da ya samu goyon bayan ‘yan majalisun tarayya da na jihohi,
A wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta, babban birnin Jihar Osun dauke da sanya hannun hadiminsa a bangaren yada labarai, Kehinde Akinyemi, tsohon shugaban ya ce tabbas gwamnatin yanzu ba ta dauki lamarin tattalin arziki ta hanyoyin da suka dace ba, wanda hakan ne ya janyo ‘yan kasar ke cikin ukuba kuma ake ta samun koma-bayan kan faduwar darajar naira.
Sanarwar ta yi bayanin cewa Obasanjo wanda ya yi wadannan maganganun a wajen wani taron ci gaban Nijeriya, hanyoyin da gwamnati ke bi da ba su kamata ba wajen tafiyar da tattalin arziki da tsaro da ya gudana Paul Aje Collokuium (tPAC) da ke Abuja.
Obasanjo ya kuma soki wadanda suke caccakar matakinsa da ya dauka kan garanbawul ga matatar man Fatakwal a Jihar Ribas, ya misalta masu kushen da cewa masu yunkurin yaudaran jama’a ne.
Ya ce, masu irin wannan kushen sun kasa tuna irin kokarin da aka yi a shekarar 2007 na ganin an gyara matuntun mai da ya yi da kuma irin zurfin tunani da ya dauka kafin aiwatar da shawara ta karshe.
A cewarsa, hanyar ci gaba shi ne zurfun tunani da aiki tukuru da gwamnati za ta yi, ba wai ta takure tunani waje guda da daukan matakan na ‘yan kankanin lokaci ba.