A sakamakon yajin aikin da kungiyar kwadagon ke ci gaba da yi a fadin kasar, gwamnatin tarayya ta sake kiran taron kwamitin bangarorin hukumar albashi da kudaden shiga da kuma biyan albashi ta kasa (NSIWC). Wannan taro da an shirya gudanar da shi da karfe 10 na safiyar ranar Talata, da nufin magance matsalolin da suka shafi sabon mafi karancin albashi.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnati ta cika da mamakin yadda ma’aikatan suka bi umarnin shiga yajin aikin tun a ranar farko. An fara yajin aikin ne bayan da kungiyar kwadagon ta fice daga taron tattaunawa a ranar 31 ga watan Mayu saboda kin amincewa da karin mafi karancin albashi da gwamnati ta yi daga ₦30,000 zuwa ₦60,000.
- NLC Ta Bukaci A Kara Wa ‘Yan Jarida Albashi, Inshora Da Fansho
- Gobe Za a Tsunduma Yajin Aiki, An Gaza Cimma matsaya Tsakanin Gwamnati Da NLC
An dai tabbatar da cewa yajin aikin ya samu karbuwa sosai a Jihohin kasar da dama a yau Litinin, lamarin da ya nuna yadda ake goyon baya ga bukatun kungiyoyin kwadago.