Rundunar Sojin Nijeriya ta yi watsi da zargin kashe jama’a da dakarunta na ‘Operation Udo Ka’ suka yi a yankin Kudu Maso Gabas, inda ta ce, zargin ba shi da tushe, ‘karya da yaudara’ ce.
Wani da ya bayyana kansa a matsayin shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Simon Ekpa, a wani faifan bidiyo, ya yi zargin sojoji da kashe ‘yan kabilar Igbo da ba su ji ba ba su gani ba a Oliver tare da jefa su a cikin kogin.
- Napoli Ta Nada Antonio Conte A Matsayin Sabon Kocinta
- Tinubu Ya Bai Wa Minista Wa’adin Kwana 2 Don Samar Da Tsarin Mafi Ƙarancin Albashi
Amma, Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya ce, sabanin rahoton na karya, bincike ya nuna cewa sojojin da ke cikin faifan bidiyon ba jami’an rundunar sojin kasa ba ne, rundunar sojojin ruwan Nijeriya ne wadanda ke gudanar da gwajin harba makamin da aka dora akan mota.
Ya kara da cewa, domin tabbatar da tsaron sauran masu amfani da hanyar da matafiya, sojojin sun dauki matakan kariya ta hanyar dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a kan hanyar, har sai da aka kammala gwajin harbin lafiya.
Ya kuma bayyana cewa, atisayen sabanin zargin, an yi shi ne a dajin yankin Kudu-maso-Yamma ba Kudu maso Gabas ba.