An gudanar da matakin karshe na gasar kwarewar harshen Sinanci wato Gadar Sinanci karo na 17, na daliban makarantun sakandare, jiya Laraba a jamiar Kenyatta ta kasar Kenya, inda dalibai 16 suka fafata.
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Kenya da kwalejin Confucius ta jamiar Kenyatta da sauran masu daukar nauyi ne suka shirya gasar, wadda ta mayar da hankali kan magana da harshen Sinanci da nune-nune basira.
- An Tsaurara Tsaro Bayan Fara Shari’a Kan Rikicin Masarautar Kano
- Xi Jinping Ya Amsa Wasikar Shugaban Jami’Ar Kean Ta Amurka
Jamian diplomasiyya da shugabannin kamfanoni da dalibai ne suka halarci gasar, wadda ta nuna yadda wadanda suka shiga gasar suka nuna kwarewarsu wajen magana da harshen Sinanci da kuma basirarsu a bangaren wake-wake da raye raye na gargajiya da kokawa da rubutu mai salon zane-zane.
Mukaddashiyar shugaban jamiar Kenyatta Waceke Wanjohi, ta ce gasar wadda ta ja hankalin dalibai daga fadin kasar, ta kara tabbatar da karfin dangantakar aladu dake tsakanin Sin da Kenya.
A cewarta, sun ga alfanun harshen Sinanci ga matasan, kuma harshen ya kawar da shingaye tare da inganta hadin gwiwa da abota tsakanin kasashen Kenya da Sin. (Mai fassara: Faiza Mustapha)